Kasashe Uku Da Aka Hana 'Yan Kasar Yin Amfani Fa Facebook Kwata-Kwata

Kasashe Uku Da Aka Hana 'Yan Kasar Yin Amfani Fa Facebook Kwata-Kwata

Kada kayi mamaki domin kaji ance akwai kasashen da aka hana amfani da dandalin sada zumunta na facebook ta hanyar blocked dinsa.

Domin a duniya rankatakab, akwai kasashe kwaya uku wadanda suka kulle damar shiga facebook wa 'yan kasar.

Mu kanmu da manyan kasarmu zasu kyauta da sun kulle mana manyan shafukan batsa, ma'ana suyi block na ip dinmu daga samun damar ziyartarsu.

Da sunyi jihadi babba.

Yanzu zaku ji kasashen da suka yi block din facebook da kuma dalilan yin hakan, domin komai baya yiwuwa sai da dalili.

1. Kasar Koriya Ta Arewa

Shugaban Kasar Koriya ta arewa wato Kim Jon Un ya kaddamar da shirin dakile amfani da yanar gizo a fadin kasarsa.

A shekarar dubu biyu da sha shida ne kasar Koriya ta arewa ta dakile shiga facebook ga 'yan kasarta, ta hanyar blocked dinsa.

Kim Jon Un, yana tsoron kar ya rasa karfin mulkinsa a kasar, shine dalilin da yasa ya dakile amfani da facebook daga kasarsa ta South Koriya.

2. Kasar Chana

Kasar Chana ma ta dakile shiga facebook ga 'yan kasarta biyo bayan wata gagarumar zanga-zanga data auku a kasar a shekarar 2009.

Zanga-zangar ta auku ne a Urumqi, gwamnatin kasar Chana ta zargi kafar Facebook akan aukuwar al'amarin, tana tunanin 'yan kasarta na amfani da wannan kafa wajen tayar da fitina a kasar.

Wannan dalili yasa suka dakile facebook gaba daya daa kasar Chana.

3. Kasar Iran

Kasar Iran yanzu hakan tana fama da rikicin siyasa tsakaninta da Kasar Amurka, wadansu lokuta wannan rikici yana kaiwa ga farmakin na'urori masu kwakwalwa (Cyber Attack).

Facebook mallakin Amurka ne, wannan dalili yasa Kasar Iran ta dakile 'yan kasarta daga shiga da kuma amfani da kafar Facebook.

Wani abin birgewa game da hakan shine: duk da sauran 'yan kasar Iran an dakilesu daga shiga da amfani da Facebook, asusun Facebook da Twitter na Kusoshin gwamnatin kasar yana aiki kwarai da gaske.

*****

Wadannan sune jerin sunayen kasashe Uku wanda suka dakile yin amfani da dandalin sada zumunta na facebook wa 'yan Kasar.

Kada mai karatu ya manta, ya yi sharhi akan wannan rubutu, sannan yayi share.


Da fatan kaji dadin sauke wannan hausa novel ko karanta wannan post?

Kayi comment da share na wannan novel ko post, sannan ka yi join din tasharmu ta telegram, duba kasa.

Leave Your Comment

0 Comments