Matsalar Saurin Inzali, Abinda Ke Kawo Shi da Maganinsa

Matsalar Saurin Inzali, Abinda Ke Kawo Shi da Maganinsa

 Assalamu Alaikum.

Da farko ina yi wa bako na barka da zuwa wannan shafi na Hausa Novels.

Saurin Inzali

Kamar yadda na zayyano a farkon rubutun nan, zan rubuta bayani dalla-dalla ne akan saurin inzali, yadda za'a maganceshi, abin da ke haifar dashi, da maganinsa.

Jinsin Mata Kala Biyu Wurin Jima'i

Binciken masana ya nuna mata na bukatar jimawa ana saduwa dasu kafin su kawo, sai dai sun kasu gida biyu.

Mata 1: su wadannan kalar matan suna da bukatar a dauki a kalla mintuna ashirin (20) ko fiye da haka ana saduwa dasu kafin su iya samun biyan bukatarsu.

Mata 2: Matan dake a sahu na biyu, basa da bukatar a dauki mintuna 20, mafiya yawanci mintuna 10 kacal sun biya.

Shin Menene Ma'anar Saurin Inzali

Saurin inzali ko saurin kawowa na nufin saukin fidda maniyi cikin 'dan takaitaccen kankanin lokaci yayin saduwa da iyali.

Masu fama da irin wannan matsalar zaka ga mutum yana fitar da maniyi cikin abinda baifi sakwanni ko minti daya ba yayin da ya shigar da azzakarinsa cikin farjin matarsa.

Matsalar saurin inzali na haifar da fushi da takaici ga ma'aurata domin tana hana miji da matarsa samun jin dadi da gamsuwa daga jima'i.

Abubuwan Dake Haifar Da Saurin Inzali Ga Maza

Dalilai ne masu yawa ke haifar da saurin inzali, daga cikin dalilab dake haifar da saurin inzali ga maza masu gida
akwai:

1. Sabon Hannu (Shiga)

In har mutum sabon hannu ne, kamar dai ango (barawo da sallama) baya bukatar karin bayani domin mafiya yawancin angwaye sune akan layin farkon dare.

Kasancewar ango bako a al'amarin saduwa ba lallai yasan yadda zai mallaki kansa ba yayin saduwa da iyalinsa, hakan zai iya haifar masa da saurin inzali.

2. Shiga Matsananciyar Damuwa

In mutum an wayi gari ya samu kansa cikin matsananciyar damuwa walau ta matsin rayuwa da al'amuranta, gidan haya ko wani abu daban.

Hakan na iya haifar masa da saurin inzali yayin da yake saduwa da iyali.

3. Jin Tsoro, Zumudi da Gaggawa

Daga lokacin da aka ce a tsorace mai gida yake walau ya karaya ko yana shakkar wani abu a rayuwa, to yayin da yaje wa iyalinsa hakan na iya haifar masa da saurin inzali.

Karanta: Sirrikan Mallakar Miji a Musulinci kuma na har abada

Ko kuma namiji ya rinka zumudi yayin da yaje saduwa da iyalinsa, wannan zumudin nasa ba zai barshi ya tabuka abun arziki ba.

Hakan na iya assasa masa saurin inzali yayin saduwa.

Ko gaggawa, domin dama ita ance aikin shaidan ce. Wannan na nufin a matsayinka na magidanci ka rinka yin gaggawa yayin kaiwa-da-komowa wajen yin jima'i.

Babu shakka hakan zai iya haifar wa da mutum yin inzali da gaggawa.

4. Basir Ko Ciwon Sanyin Mara

Basir kansa in yayi kaka gida a kwankwason namiji na iya haifar masa da saurin inzali, yayin da yake saduwa da iyali.

Haka ma Ciwon Sanyin Mara, yana da illa kwarai ga lafiyar 'da namiji, domin yana haifar da saurin inzali, yana haifar da kankancewar gaba.

Kurajen gaba, kaikayin gaba da sauran cututtuka da Allah ne kadai masaninsu.

In har kana da yakinin kana dauke da ciwon sanyin mara, ka yi kokarin lalubar gangariyar maganin gargajiya ka gwada.

Allah ya datar da mu.

5. Gajiya, Ko Daukar Lokaci Ba'ayi Jima'i Ba

Gajiya na daya daga cikin abubuwan dake haifar da saurin inzali ga maza, mafiya yawancin masu hada-hadar kasuwanci sun fi fama da ita.

Yana da kyau ka rinka baiwa kanka lokaci kana 'dan hutawa domin karawa kanka lafiya.

Daukar Lokaci Ba'ayi Jima'i ba shima yan kawo saurin inzali, lokacin da aka fara jima'in, yana da kyau a kiyaye.

6. Rashin Cin Abinci Mai Gina Jiki

Akwai abinci kala-kala daga kan masu kara lafiya, har zuwa ga masu kara karfin gaba, yawan maniyi da sauransu.

A matsayinka na magidanci yana da kyau ka rinka cin abinci mai gina jiki, domin hakan zai taimaka maka wajen jimawa kana jima'i da matarka.

7. Taruwar Mataccen Maniyi a Mara

Shima wannan tamkar ciwon sanyin mara ne, ka lalubi magani kasha wanda zai wanke maka mararka.

Hakan shine mafita.

8. Yawan Fushi ko Tashin Hankali Tsakanin Ma'aurata.

Idan har ya kasance tsakanin ma'aurata ba'a jituwa zai kasance kowanne ba ya cikin shauki yayin saduwa.

Wanda ba iya namiji bama hatta macen hakan na iya haifar mata da saurin inzali.

9. Rashin Motsa Jiki

Anzo inda tafi tsami, wato motsa jiki, zaka ga yayin da mutane musamman hausawa, mutum yana matashi yana motsa jiki.

Amma daga ya samu 'yan shekaru da aure, sai ya dena, dan gudun safiyar ma ya dena, 'yar ball din ma ya dena.

Rashin motsa jiki na haifar da matsaloli marasa adadi, ba iya saurin inzali ba, akwai wasu cuttukan ma daban.

Yana da kyau ka rinka yawan motsa jiki koda na minti 30 ne a rana, domin zai kara maka lafiya da zama fitted.

Wadannan sune guda 9 daga cikin abubuwan dake haifar da saurin inzali ga 'da namiji, ba iya su kenan ba.

Kuma akwai wadanda ake haifarsu da matsalar saurin inzali, ga wanda yake da ita tun daga haihuwa zaifi kyau yaje ya ga likita.

Yadda Ake Magance Saurin Inzali Ba Tare Da Anyi Amfani Da Magani Ba

Domin magance saurin inzali ba tare da kasha magani ba, ga wasu muhimman shawarwari 4, indai kayi amfani dasu za ka amfana.

  • Ka rinka yawan motsa jiki
  • Ka rage yawan shan kayan zaki kamar na minti, kafi zabo, alewa da sukari
  • Ka rage cin kayan maski wadanda ba dangin kifi bane ko nama.
  • Ka fara gabatar da wasanni tsakaninka da matarka kafin jima'i, domin yin hakan Sunnah ne kuma yana taimakawa wajen rage saurin inzali.

Ingantaccen Maganin Saurin Inzali

Na tabbata in dai ka samu damar karanta dukkanin bayanan dake sama kasan akan me muke magana.

Yanzu zanyi kokarin wallafa sahihan magungunan saurin inzali guda 2.

Da fatan zasu amfaneka, kada ka manta kayi sharhi a wannan rubutu nawa.

1. Man Kanumfari ko Na'a Na'a

Ka samu man kanumfari ko kuma man na'a na'a sai ka samu ruwan dumi ka wanke azzakarinka dashi sosai.

Sannan ka kawo man kanumfarin nan ko na na'a na'a sai ka shafe azzakarinka dashi sosai amma banda kofar da fitsari ke fita.

Ka yi hakan mintuna kadan kafin ka tara da iyalinka, da yardar Allah za'a dace.

2. Citta, Masoro, Kanumfari Da Zuma

Ka samu:

  1. Masoro
  2. Kannufari
  3. Citta (danya mai yatsu)
  4. Zuma.

Yadda ake hadawa: ka samu citta ka daka ta, sai ka ka kawo wannan masoro da kanumfarin sai ka hada su a wani kwanon ka zuba ruwa ka dafa sosai ya dahu.

Sai ka kawo wadatacciyar zuma ka zuba a ciki, bayan ka sauke shi yana turirin nan.

A karshe sai ka rinka sha kofi daya da safe, daya kuma da yamma.

Da yardar Allah za'a dace.

****

Wallafawa: Abba Abdullahi Garba.

Gargadi: ban gwada daya daga cikin magungunan gargajiyar nan ba, amma in har saurin inzali shine matsalarka a shawarce kawai ka gwada.

Bana da garanti akan yana yi, domin ni bana da bukatarsa sabida har yanzu 0 ne ni, dan haka ka dauki kasada ka jarraba.

Allah yasa mu dace.


Da fatan kaji dadin sauke wannan hausa novel ko karanta wannan post?

Kayi comment da share na wannan novel ko post, sannan ka yi join din tasharmu ta telegram, duba kasa.

Leave Your Comment

0 Comments