Kar Ka Shiga Sabgar Damafarar Yanar Gizo, Irinsu InksNation da Income Programs

Kar Ka Shiga Sabgar Damafarar Yanar Gizo, Irinsu InksNation da Income Programs

To da farko ina yi wa mai ziyartar wannan shafi barka da zuwa.


Naji dadin sake kasancewa tare da kai a cikin wannan sabon rubutu nawa mai taken "kar ka shiga sabgar damfarar yanar gizo", irinsu InksNation da Income Programs.

Yana daya daya daga cikin gargadin da zan iya yi maka, a matsayi na na wanda baya son a cuceka, musamman a yanar gizo.

***

Duniyar nan tamu cike take da maha'inta, macuta, mazambata da 'yan damfara.

Kuma indai ta fannin yanar gizo ne, mafiya yawancin su suna bullo wa ne daga kudancin Kasar Najeriya.

Shin su waye suke bata mana suna, cikin gida da wajen Najeriya? Malam wasu lalatattun matasan kudancin Najeriya ne.

Da farki akwai wata hanyar damfara da ta jima tana tashe ana kiranta da "Income Program".

Wato shi income program in har ka taba shigarsa bai wuce irinsu NNU INCOME, NEWSPAY, ENIGERIA, IBTFORUM da sauransu.

In mai karatu bai manta ba, zai ji ana ta rudarsa da ya saka naira dubu 1000 zai rinka samun sama da naira dubu 30, 0000 duk wata.

Wasu ma za ka ji suna cewa duk sati za ka rinka samun irin wadannan makudan kudade.

Kuma fa ba wani abin azo a gani zaka rinka yi musu ba.

Zaka rinka post, comment, share da kuma yin likes na posts a shafinsu ne kawai.

Hakika an zalunci mutane da dama ta wannan salon damfarar, dalibai da dama ma sun rasa kudaden makarantarsu.

Asarar dai ba'a magana.

Saboda haka ko yanzu kaji wani abu da zaka rinka comment, ko share na post a rinka biyanka wallahi cuta ce.

Kada ka shiga, in kuwa ka ki ji, to fa ba za ka ki gani a kokon shanka ba.

***

To kwana-kwanan nan sai ga wata sabuwar damfara mafi muni ta bullo daga wani bayarabe.

Ba munki shi bane, saboda shi bayarabe ne, amma ko bahaushe ne yazo da ita dole mu fade shi.

InksNation

Tsari na kudin CryptoCurrency wanda da Allah (S.W.T) ya tabbatar da wannan tsari na InksNation da ya zama babban cigaba ga 'yan Afirka, mutanen Afirka dama na duniya baki daya.

To sai dai.

Shi wannan bayarabe mai suna Amos Omotade, madadin ya kafa wa jama'a wani abu mai kyau da zai amfane su, sai ya buge da kafa sabgar damfara.

Madadin ya zama mai magana daya sai ya zama makaryaci.

Zan so mai karatu ya sauke littafjn Ibrahim Abubakar Mubi mai taken "InksNation Alamomin Tambaya?" ya karanta domin fahimtar menene inksnation da inda ya dosa.

Ko nawa ka saka a inksnation, muna nan da kai zaka ji lokacin da amos zai yi batan dabo.

A nemeshi a rasa.

Mutumin da yayi ikirarin sun kawo tsarin da zai raba mutanen Najeriya da talauci.

Sai gashi yau a cikin panel na members, shi da kansa yake neman temakon kudi (donate).

Ga mai hankali:

*Shin ta yaya tsarin InksNation zai fitar da mutane daga talauci, alhalin su kansu bara suke wurin jama'a ? *

* Shin in har gaske ne inksnation, menene dalilin da yasa cryptocurrency na duniya yaki yi masa rajista da bashi lasisi ?. *

* Shin menene dalilin da yasa duk karairayin Amos bai cika su ba, game da cigaban InksNation?. *

* Shin me yasa Amos bai taba cika alkawarin daya dauka game da turawa mutane kudin da yace duk wata zai rinka tura musu shi ba 100% ?. *

Muna da tambayoyi masu tarin yawa akan InksNation wadanda sai wanda ya jima cikin tsarin ne zai iya amsasu.

A shawarce.

Kana son kanka da arziki kada ka shiga sabgar damfarar InksNation.

Domin zata bare da kai, kayi asara, kai ba sadaka kayi ba ba kyauta kayi ba, ba kuma wani amfani kayi da kudinka ba.

Idan kunne yaji, aljihu da aninai sun tsira, kuma an huta da bakin ciki.

***

Wassalam mu huta lafiya.

Da fatan kaji dadin sauke wannan hausa novel ko karanta wannan post?

Kayi comment da share na wannan novel ko post, sannan ka yi join din tasharmu ta telegram, duba kasa.

Leave Your Comment

0 Comments