Karanta Littafin Epub a Wayarka Da Lithium Epub Reader Pro Apk

Karanta Littafin Epub a Wayarka Da Lithium Epub Reader Pro Apk

Shin ka yi download din hausa novel wanda ya ke a Epub format daga Top Hausa Novels?.

In har ka yi download din sa, ina maka maraba da ziyaryar wannan shafi.

Da yardar Allah a cikin wannan takaitaccen rubutu nawa zan maka bayani akan yadda zaka karanta littafi a epub format ta hanyar amfani da lithium reader app.

Da dama daga cikin masu karatun littafan hausa musamman masu yinsa a waya, sun san okadabooks.

To, su littafan okadabooks a epub ake wallafa su, in har kana son karatun su sai kana da epub reading app a kan wayarka.

Daga cikin kalar litattafan da mu ka sha alwashin kawo muku akwai wadanda suke a epub format.

Hanya mafi nagarta ta karanta littafi a epub ita ce, ta hanyar amfani da lithium app.

Ni nan na yi amfani dashi, kuma yana da dadin karatu, ga dark mode, manyan bakake, resume daga inda ka tsaye da sauransu.

LITHIUM EPUB READER REVIEW

Application ne na wayar android,  za ka iya samun sa a google playstore, sai dai muddin kan a son kaji dadin amfani dashi.

To ka nemi premium version din app din.

Ta yaya zaka same shi?

Ka yi search na "Lithium Pro Apk ko Lithium Premium Apk" a google ko bing za ka same shi.

Domin na saukaka maka samunsa, zan baka adireshin da za ka dauko wannan application.

DOWNLOAD LITHIUM EPUB READER PRO APK

Epub reader, lithium app yanzu haka zaka iya dauko sa daga idan ka latsa button din dake kasa.

Download Lithium Epub Reader Pro Apk

Bayan ka dauko shi, sai ka bude app din ta hanyar yin installing dinsa akan wayarka.

YADDA AKE AMFANI DA LITHIUM PRO APK

Bashi da walahar amfani, da zarar ka dauko littafinka a epub format, indai yana kan wayarka.

Ka bude lithium app, ka taba digo uku na tsaye daga saman hannun damar wayarka, zaka ga ya nuno maka menu.

Na farko zaka latsa, wato refresh, nan take zai kwaso duk littafan dake kan wayarka in dai a epub format suke.

In Zaka Kunna Night Mode

Ka bude littafinka a cikin lithium app, za ka ga wata A mai giya kusa da digo uku (:) da kuma alamar rariya.

Ka na taba nan, menu zai bayyana, za ka ga "Theme", to nan za ka taba irin kalar hasken background din da kake so.

Nana take zai koma dai-dai yadda kake so.

***

Ina da yakinin cewa, in har ka ci gaba da bincika app din lithium za ka ga yafi kowanne pdf reader dadin karatun littafi.

Kada ka manta, kayi comment sannan kayi share na wannan post.


Da fatan kaji dadin sauke wannan hausa novel ko karanta wannan post?

Kayi comment da share na wannan novel ko post, sannan ka yi join din tasharmu ta telegram, duba kasa.

Leave Your Comment

0 Comments