Shawara Zuwa Ga Sabuwar Amarya

Shawara Zuwa Ga Sabuwar Amarya

Gaisuwa mai tarin yawa tare da fatar kina cikin koshin lafiya!.

Ya aka ji da dawainiyar shirye-shiryen wannan buki namu mai alfarma da dimbin tarihi a cikin zukatanmu da kuma zukatan masoyanmu? Allah Ya sa komai na tafiya kamar yadda kike bukatarsa. 

Ina fatar Baba da Inna suna lafiya.

Ya ke wannan amarya mai dimbin farin jini da tarin albarka, na san za ki yi mamakin ganin wannan wasika a daidai wannan lokaci, to ba komai ba ne, ina so ne kawai in yi amfani da wannan damar domin kara tunatar da ke abin da kika riga kika sani.

Saboda ke mai ilimi ce da kuma cikakken hankali.

Godiya ta tabbata ga Allah da Ya ba ni ke.

Ki sani, ban nemi aurenki ba har sai da na tabbatar da cewa, ke mai tsoron Allah ce, kuma mai kokari wajen bin dokokin shari’a. 

Saboda haka na san ban zabi tumun dare ba. 

Wannan kuma ba shi yake nufin na manta da tsabar kyawon halittar da Allah Ya halicce ki da ita ba, ba kuma shi ke nufin na manta da nasabar gidanku da arzikin da kuke da shi ba!.

Sai dai, ba su ne gabana ba idan aka kwatanta da babban makasudin da ya sa na nemi aurenki.

Manzo Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi ne ya ba ni shawara da kansa a cikin lamarin neman auren nan, ashe ko tun da na bi shawararsa, ba ni da sauran wani tsoro. 

Na san na gama dacewa.

Yanzu kin ga auren Ladidi da Musa, ya samu cikas ne sanadiyyar zabin kansa da ya bi a wajen yin sa. Domin ya auri Ladidi ne saboda wasu ababe daban, wadanda a lokacin da Manzon Rahama ke ba mu shawara, shi bai dauki shawarar ba, sai ya bi kyale-kyale.

Allah Ya ja zamaninki. 

Duk fadin duniyar nan da kewayenta idan tana da shi, ki sani babu wata wadda nake gani a gabana face ke! Babu wata ’ya mace da nake yi wa fatar alheri kamar ke. 

Also Read: Kana Son Dena Istimna'i? To Kaga Hanyoyin Da Zaka Bi Domin Dena Istimna'i

Saboda wannan dalili nake son in sanar da ke wasu ababe da za ki kiyaye mini su a gidana, wadanda kiyaye su ne zai kara ba ni damar sauke hakkinki da Allah Ya dora mini kuma in samu cikakkar damar kyautata miki fiye da tunaninki.

Na farko dai, ki ‘kara kaimi wajen bautar Allah da kuma yin da’a ga ma’aikinsa Annabi Muhammad (SAW). 

Abu na biyu kuma, ki mutunta ni tare da daukacin ’yan uwana, musamman mahaifiyata. 

Idan kin yi wannan, lallai kin gama mini komai. 

Da ma tun ranar da kika amince da ni a matsayin abokin rayuwa, kin yi mini komai.

**** Daga Watsapp ****

Wannan rubuta, ba Abba Abdullahi Garba ne ya rubuta shi ba, mun sameshi ne daga wani dandali a watsapp na hausa novels.

Muna godiya.


Da fatan kaji dadin sauke wannan hausa novel ko karanta wannan post?

Kayi comment da share na wannan novel ko post, sannan ka yi join din tasharmu ta telegram, duba kasa.

Leave Your Comment

0 Comments