Azumin ILU

Azumin ILU

 πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

*AZUMIN ILU*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

*MAMAN MAMY ce nace Ku huta*✍

*sadaukarwa gareki aminiyata Kawar Alkhairi ga nawa goron azumi tunda ban sayi sugar da gero ba*πŸ˜†

A guje ya shigo gidan har yana karo da tumakan dake tsakar gidan...shigar jikin shi kawai zaka kallah kasan cewa ILU ko a kauyen su babba ne wurin shirme da shiririta.. Wani zabgegen wando ne jikin shi mai irin felar nan na mutanan da ....ga wata bajejejiyar Riga wadda ake kira da Yar shara yasha wani kafcecen glass da ido dayane kawai ke gani ........kai fans ILU fa babba ne a kauye an su ..cikin nan nasa kato dashi kamar shi kadai ake cidawa gidan ......

Haba ILU baka gani ne zaka shigo mana haka ...ko dai biyoka akayi ne.... Wata Yar tsohuwa ta fara masa fada .....kai dai ba ranar da zakayi hankali ILU...... Kinga iya niba wani dogon zance na tambaye ki ba ....wai jita jita naji agari cewar gobe ne zaa tashi da azumi acan santar na kyallu na jiyo.....

Yar dariya iya tayi ...kai ILU amma bakada dama ...yanzu murnar zuwan azumince ta da ka shigo haka.... Eh da gaske ne in Allah ya amince gobe ne zaa tashi dashi sai kazama cikin shiri .....

Wayyo Allah wayyo na shiga ukku na lalace shi kenan lokacin mutuwa ta yazo na shiga ukku ni ILU ...ya fada tare da dukewa kasa yana matso kwalla.....

Kai ILU lafiyarka kuwa ....yanzu AZUMIN ne kakema wannan ihun ...oh ni salame Allah na gode maka......

Haba iya ba dole inyi kuka ba... Kina gani da safe Kofi gudu nake sha na koko inci dumamen tuwo kwano guda ....da rana ta daga zani rumfar shehu inci awara ta nera Dari... Da rana in kwashi kwano guda na abinci ...kafina mangaruba inbi na sauran yaran gidannan in cinye in malam ya dawo yaci ya rage ya bani... Da daddare bayan naci tuwo kwano agida saina fita na ni almajirai bara inkara cika cikina.... Yanzu sai ace nida abinci sai anyi sallar magrib ai lokacin na mutu kawai.....

Malam ne ya babba ke da dariya dama tun sadda ya shigo ILU ke bayani... Itama iya dariyar takeyi .....ato shiyasa Nike maka fadan cin abinci amma bakaji... Kome na noma a gidannan Kaine ke cinye shi ...nikam nayi murna da zuwan WATAN RAMDAN wata mai falala da rahama kai yanzu ILU duk bazaka tuna da niimomin da zasu sauko ba sai ta abinci kake ......malam ya fada dariya cike da cikinsa......

Cikin kuka ILU ke fadin wllh malam nayi murna da zuwan shi ...ni yauma zan fara nawa ...amma can cikin zuciyar ILU ba haka abin yake ba tunanin yunwa kawai yakeyi .....uhm kai dai kasani azumi ba fashi sai kayi talatin cif ko zaka mutu kaji dai abinda nace maka ...suma mutanen kauyen sun huta da fitinarka na Dan wani lokaci.... Malam ya fada tare da shige wa cikin dakinsa yana dariya...

Iya CE ta dubeshi.. Ni kaga da wannan kukan da tashi kayi ka amso min nikan tuwo shagon talle daya fiye maka ...insamu inmana abincin sahur....

Jiki ba kwari ILU ya mike yayi waje yana baje fantalon wandonsa....

Duk inda yaga gungun mutane sai ya tsaya yace... Ato WATAN RAMADAN gobe sai Ku shirya don yunwa badai Kanwar Babar mutum bace bare ta raga masa

Sai mutane suyi dariya suce ..ILU da kanka kake ...mai cikin Zane sai akwashe da dariya shikau gogan ko ajikinsa ...

Maman MAMY CE nace Ku huta don AllahπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜†πŸ˜†

AZUMIN ILU*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

        *peg 2*

*MAMAN MAMY CE*✍

*karfa acika ILU da dariya saboda bashi kadai bane akwai masu tsoron yunwa*πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

*gaisuwa ga yan BRRILIANT*⚜hantsi lekadan kowa

Ahaka yaje ya dakko nikan ya dawo sai shela yake gobe azumi kamar maigari ya sashi πŸ˜‚

Yana dawowa sallar magriba ya tule kasa kusa da Kanwar shi asabe .....dubanta yayi wai iya bata gama sanwar bane .....dubanshi tayi kai ILU kayi mata hakuri yanzu zata gama aci ci ...ko kallon inda take bai kara yi ba yacigaba da kallon inna na tuka tuwo .....

Loma yake kamar ya kwana bai Ciba ....in kaga tuwon da aka jibgomasa saika rantse da Allah na mutum ukku ne ........

Iyah...Allah dai yasa kin yi tuwon nan da yawa saboda sahur ...kinsan sai naci Wanda ya linka wannan saboda kar inji yunwa sosai ....kinga salon way on nawa ko asabe ya kalleta tare da afka wafceciyar loma bakinsa yana side miyar da ta biyo ta bayan hannunsa .....

Dariya asabe tayi ba wani wayo ILU ....duk wannan tumbin da kake fama dashi saiya sabe.. Ta ida maganar tana kumshe dariya ....shidai baice komai ba yaci gaba da saka lomar tuwonsa baki... Aishi komai dai dai yakeji.....

Kade kaden da yaranmu suka saba lokacin azumi domin tada sahur.... To haka abin ya kasance a kauyen Ku suma.....malam ne ya hau tashin ILU dake kwasar bacci ......

Jamaa kuzo kuga uban dumamen tuwon da ILU ya kwashe su malam kallonsa kawai suke ....asabe kam kagara tayi gari ya waye taga yadda ILU zai kasance......

Washegari yana dawowa sallar asuba ya koma ya kwanta ...cike da tunanin yau ba batun shan koko ....

Misalin 10 na rana ya tashi ...cikinsa ya fara kiran ciroma ...gashi yana tashi yaje yayi uban tulin kashi kunga kenan ba magana.

Ragwaf ya dawo ya zauna karka shin bishiyar bedi dake tsabar gidan yana kallon yadda tinkiya ke kwasar dusa abinta..... Iya ya kalla dake shara...

Wai iya meyasa su tumakai basu yin azumi ne yanzu jibi yadda shegiya r tunkiyar nan ke cin dusa kamar da gayya takeyi saita wani kalle ni saita cika baki don inji haushi .....ya fada yana Harar tunkiyar da batasan Allah ma ya aje shi ba ....

Dariya iya tayi sosai ....ILU kenan kai dai ka tashi kayi wanka ka fita can wajen abokanka Ku cigaba da salatin annabi ...kar yunwa tasa ka mazgar min tunkiya nasan halin ka ......

Mikewa yayi tare da sakin tsaki ......yunwa nata kwalkwalar sa ....jibarta da kunnuwa fala fala... Wai da tunkiyar yake.

Ita dai iya batace komai ba saboda tasan abinda ke damunsa...

Afujajan ya fito wankan ya samu wata Yar jallabiya ya sagala da wata doguwar cafzaha yayi waje .....saura kadan ya bige asabe da sauri ta matsa tana dariya ...

Santar na kyallu ya nufa inda abokansa ke zama.... Tun daga nesa suka hau yimasa dariya suna cewa....

Yayi ILU n iya mai cikin Zane yunwa dai ba Kanwar  babarsu mutum bace bare ta raga masa...

Wani wahalal Len yake yayi ...ya nemi wuri ya zauna ya fara Jan cazbaha yana kallonsu baice masu kanzil ba .....dariya basiru yayi aaa ikon Allah mutumenfa da gaske n gaske ibada yake Ku kalla salati yakeyi ILU ILU ILU na malam .....gaba daya suka babba ke da dariya...

Kudai zauna nan ...ILU ya fada a wahalce yana zare idanu ....

Anata fira ILU kam anyi tsit sai salati akeyi... Can su kaga ILU ya hau lumshe idanuwa... Aa ILU bacci zakayi basiru ya tambaya....

Aa basiru babacci zanyi ba bari dai agama min hisabi cikin cikina da alama hanjina basu da kwari ......

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

*AZUMIN ILU*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

         *peg 3*

*MAMAN MAMY CE*✍

*Allah ka sada mu da alkhairan dake cikin wannan wata mai albarka Allah ka bamu ikon yin duk wasu ayyuka masu lada acikin wannan wata na RAMADAN*πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™

Dariya suka sa masa gaba daya ....sannan sukaci gaba da hirarsu akan abinda ya shafi watan na RAMADAN .....ahaka har aka kira sallar azahar ..ILU kam na jinsu amma ko kallonsu baiyi bare yasa baki ....

Basiru ne ya dubeshi mutumen ankira sallar azahar ka tashi muje muyi sallah sai ka wuce gida kadan huta .....duk cikin dariya yake maganar....

Kamani basiru wllh ashirin ashirin Nike ganinku ...ILU ya fada yana kyafta idanu... Dariya sukasa gaba daya ...ahaka suka kamashi suka nufi masallacin mai gari ....kamar Wanda bai lafiya ...duk Wanda yace lafiya ILU sai yace ...yunwa Ai ba Kanwar babata bace bare ta ragamin sai mutane suyi dariya ..suce da sauran ka ILU tunda bakin bai mutu ba...

Sallah akeyi amma liman sai jawo dogayen surori yake ....kafafuwan ILU rawa kawai suke ...saura kadan ya sallame sallar yayi tasa shi kadai ...hawaye kam wani nabin wani ga wata rana mai zafi da akeyi garin....

Ana kammalawa yayi kwance yana lumshe idanu... Wllh basiru liman mugu ne dayake ya lura da yanayi shine yake Jan dogayen surori ...Wanda ya kara bin sallar shi ..πŸ˜‚

Da kyar basiru ya gimtse dariya ya samu yayi addua ...sannan ya dubi ILU kayi addua kuwa mutumen kake gulma ...kuma ba kyau gulma ana azumi kai ko baa azumi gulma ba kyau .....

Nayi addua mana basiru nace Allah ya nuna min asha ruwa ..wllh yau abincin da zanci ba karami bane ....kuma ni ba gulma Nike ba gaskiya ce ....

Ahaka dai suka rakoshi gida sai ruwan balai yake ma liman kamar shi yasa shi yin azumin ...su kau ba Wanda ya kula shi saboda kowa yasan Matsalar shi ......

To ILU sai anjima mun biyo maka zuwa waazi n da malam zaiyi kafin faduwa r rana..... Kar Wanda ya biyo min kuje kawai ni naje idan ranar ta fadi Ai inaga duk dayane ko... Ya fada yana hararar su ....aa yi hakuri malam ILU abin bana zafi bane...

Na zafin ne ...shin malam din ba ubana bane innaga dama sai ince ya yimin waazin cikin gida ba shikenan ba... Ya shige cikin gida yanata ruwan balai... Abokan kuma suka juya suna masa dariya ...

Yana shiga sukaci karo da asabe zata fita.... Wani wawan bugu ya kai mata cikin zafin nama ta kauce tana dariya ....waike bakida hankali ne baki ganin mutane ...yi hakuri ILU ba gani ba ta fada tana gimtse dariya....

Wata uwar harara ya gallara mata yayi gaba yana kallon iya dake sama dabbobi abinci... Ga matsayatan da suka fi kowa cin abinci ....amma sai ace ILU ya cika cin abinci ...ga sunan yini kike basu abinci ....iya CE ta dago tana murmushi..

Haba ILU ya zaka hada kanka dasu ...sufa dabbobine kai kuma mutum ne .....eh naji ni mutum ne amma Ai yunwa duk iri daya CE kuma duk abinci abinci ne... Haka kawai sai adameni da su dabbobi ne ...ya wuce dakin shi yana tijara..... Malam ne ya dubeta dake can gefe yana lazimi...

Ki daina biye masa azumi ne dai sai yayi talatin cif koda yunwar zata kashe ka ...katon banza bai aje komai ba sai katon ciki.....

Ana kiran sallar laasar ne malam ya leka dakin shi ....ILU tashi kayi alwalla mu tafi masallaci ....malam ka yafeman mutuwa zanyi ILU ya fada yana yan kwalla ....eh Ai dama kullu nafsin zaikatul maut dukkan mai rai mamaci ne ....kazo kayi sallar sai ka dawo ka mutun tunda lokaci yayi ......

Mikewa ILU yayi yana fadin ...eh dama Ai ka kagara in mutu tunda kace ina cinye maka hatsin daka ke nomawa ...to ka daina murna saina ci abinci sosai a duniya zan mutu ...oh ni ILU Ashe anyi Sukuti aga na mutu ahau murna to ina nan ......

Shidai malam murmushi kawai yayi ya wuce gaba ...inka gama shawara da mutuwar ka fito mu tafi masallaci saura ka batamin lokaci .......

*muje zuwa*

             *labarin ILU*

[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*


πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

*AZUMIN ILU*

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

       *peg 4*


*MAMAN MAMY CE*.....

*hhhhhh ILU na wuta ina binshi da gas*

Ahaka ya gama surutansa ya  tashi jiri na dibar shi ya yi alwalla idanuwansa har wani lumshewa sukeyi saboda tsabar yunwa .......

Ahaka suka tafi masallacin sai rangaji ya keyi shi kau malam murmushi kawai yake yi ....wani bangaren kuma tausayin ILU yakeji sosai saboda yadda yayi sabo da abinci kamar jaki

Ana kammala sallah ILU ya baje yana ta maida numfashi ...Nan take jamaa suka baibayeshi suna sallalami ....da yawansu dariya suke masa saboda sun San abinda ke damunsa  

..malam ne ya iso da sauri 

Sannu ILU bakada lafiya ne... Daga kai kawai ILU yayi ya kasa cewa komai... Maigari ne ya dubi malam... Gaskiya malam ILU ya aje AZUMIN nan tunda bazai iya kaishi ba shiga addinin Allah saukine dashi ko ba yanzu ba sai ya rama tunda lalura CE... Shiru malam yayi yana kallon ILU dake wani kara fitar da numfashi shidai yasan halin abinsa da anbi ta tashi da an kyale ILU yakai AZUMIN nan .....mutane ne suka dinga magana akan abar ILU ya aje AZUMIN ...ba da son ran malam ba ya amince ya koma gefe ya yi zaman shi ganin yadda zaa kaya da ILU n malam .


Maigari ne ya Ciro 


Da fatan kaji dadin sauke wannan hausa novel ko karanta wannan post?

Kayi comment da share na wannan novel ko post, sannan ka yi join din tasharmu ta telegram, duba kasa.

Leave Your Comment

0 Comments